rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Myanmar Birtaniya Bangladesh

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Birtaniya ta bukaci gudanar da bincike a kisan Rohingya

media
Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya Boris Johnson tare da Musulaman Rohingya a Myanmar © Reuters

Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya Boris Johnson ya bukaci gudanar da bincike mai zaman kansa domin gano wadanda suka aikata aika-aika kan Musulmai ‘yan Kabilar Rohingya a kasar Myanmar.


Johnson wanda ya ziyarci kasar, ya gana da jagorar gwamnatin kasar Aung San Suu Kyi wadda kimarta ta zube a idon duniya saboda yadda ta kawar da kai lokacin da ake cin zarafin dubban ‘yan Rohingya.

Sakataren ya bayyana cewar, ya bukaci hukumomin kasar da su gudanar da bincike domin hukunta duk wanda yake da hannu a cin zarafin.

Kungiyar agaji ta Reporters Without Borders ta ce, akalla ‘yan kabilar Rohingya dubu 6 da 700 aka kashe lokacin da rikicin ya barke, yayin da sama da dubu 750 suka nemi mafaka a Bangladesh.