Isa ga babban shafi
Iraqi

Har yanzu Al-bagdadi na raye - Iraqi

Ma’aikatar cikin gidan Iraki ta ce har yanzu jagoran kungiyar IS Abu Bakr al-Baghdadi na a raye, kawai dai ya samu rauni ne sakamakon wasu hare-hare ta sama, sannan aka yi jinyar sa a wani asibiti da ke cikin kasar Syria.

Dama wani binciken Amurka cikin watan Satumba ya nuna shakku kan yiwuwar kisan shugaban kungiyar ta IS Abu Bakr al-Baghdadi.
Dama wani binciken Amurka cikin watan Satumba ya nuna shakku kan yiwuwar kisan shugaban kungiyar ta IS Abu Bakr al-Baghdadi. 网络。
Talla

Jaridar gwamnatin Iraki As-Sabah, ta ruwaito ma’aikatar cikin gidan na cewa, Al-baghdadi na ci gaba da fakewa ne a yankin Jazira da ke arewa maso gabashin Syria.

A ranar 16 ga watan Yunin 2017 ne Rasha ta ce ta na da yakinin cewa dakarunta sun kashe jagoran kungiyar ta IS Abu Bakr al Baghdadi da ke da’awar jihadi a Syria da Iraqi a wani hari da suka kai a Raqqa.

Sanarwa Rashan ta ce akwai tabbacin al-Baghdadin na cikin wadanda suka hallaka yayin wasu jerin hare-hare ta sama da dakarunta suka kai kan tawagar ta IS ranar 28 ga watan Mayu ciki har da manyan kwamandojin kungiyar IS fiye da 30 da kuma sojinta fiye da 300.

Sai dai kuma dama wasu bayanai da Amurka ta fitar ranar 2 ga watan Satumba ta ce babu tabbacin ikrarin na Rasha ya zama gaskiya duk da cewa an rabu da jin duriyar jagoran kungiyar ta IS.

Rahoton da Janar Stephen Townsend, wani babban kwamandan sojin Amurka ya Fitar, ya ci karo da ikirarin ma’aikatar tsaron Rasha na cewa, sojinta sun halaka al-Baghdadi, inda rahoton ya nuna cewa al-Baghdadi yana boye, a daya daga cikin yankunan da ke kan iyakar Iraqi da Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.