rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka ISIL Syria

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Amuka ta ce yanzu aka fara yakar IS a gabas ta tsakiya

media
Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson, ya ce dole ne a zage kwanji don ci gaba da fatattakar mayakan na IS la'akari ga hadarinsu ga kasashen yankin gabas ta tsakaiya dama duniya baki daya. 路透社。

Sakataren Tsaron Amurka Rex Tillerson ya bukaci kasashen da ke kawancen yaki da kungiyar IS da su kara kaimi, inda ya ke cewa murkushe mayakan a filin daga ba wai kawo karshen yakin bane. Tillerson ya bayyana hakan ne a wajen wani taro da suka gudanar a kasar Kuwait.


Sakataren tsaron Amurkan ya bukaci kasashen da ke kawance da su a yakin da su ke da kungiyar IS a arewacin Syria , da su kara azama ganin yadda hare haren Turkiyya kan Kurdawa ke kawo musu cikas da koma baya.

Tillarson wanda ke jawabi a taron ministocin tsaron kawancen da ake a  Kuwait, ya ce kawo karshen IS a Syriya da Iraqi baya nufin an kawar dasu dun gurungun ba ne akwai sauran aiki gabansu.

Acewar sa, kungiyar IS za ta cigaba da zama babbar barazana a yankin na gabas ta tsakiya, da kuma sauran kasashen Duniya.

Tun cikin watan jiya ne dai Turkiyya ke luguden wuta kan mayakan Kurdawan Syriya da ke samun goyon bayan Amurka, abunda Amurkan ke bayyanawa da matukar komabaya.

A batun hare haren da Saudiyya ke jagoranta kan Yamen kuwa Sakataren tsaron na Amurka ya ce kasar sa za ta yi duk mai yiwuwa don sasanta sabanin, lura da barazanar tsaron da rikicin ya kawo yankin Gulf.