rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa Syria Majalisar Dinkin Duniya Rasha

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Faransa za ta kaddamar da hari a Syria- Macron

media
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya nuna damuwa kan harin makami mai guba a Syria REUTERS/Benoit Tessier

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce, kasarsa za ta kai harin jiragen sama kan dakarun Syria muddin aka tabbatar da cewar, sun yi amfani da makami mai guba kan fararen hula.


Macron ya shaida wa manema labarai cewa, Faransa ba za ta lamunce da kai irin wannan hari ba, saboda haka muddin aka tabbatar da gaskiyar lamarin, to lallai za su kai harin in da ake kera makamin mai guba.

A cewar Macron, babu shakka cewa, ya shata layi dangane da harin makamai mai guda.

Sai dai ya ce, ya zuwa yanzu babu wata shaida da ke nuna cewa jami’an sun yi amfani da makamin kan fararen hula.

A wata zantawa da ya yi ta wayar tarho da takwaransa na Rasha, Vladmir Putin, shugaba Macron ya ce, ya damu matuka kan rahotannin da ke cewa, a 'yan makwannin nan an kai sabbin hare-haren makami mai guba kan fararen hula a Syria.

Gwamnatin Syria ta sha musanta amfani da makami mai guba tare da fadin cewa, ‘yan tawaye kadai ta ke ragargaza.

Yarjejeniyar kasa da kasa da Syria ta sanya wa hannu, ta haramta amfani da makami mai guba, yayin da Majalisar Dinkin Duniya ke cikin sahun masu caccakar gwamnatin kasar kan amfani da makamin.