rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kuwait Iraqi Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kuwait za ta ba da bashin dala biliyan 1 don gina Iraqi

media
Sarkin Kuwait Sheikh Sabah Al Khaled Al Sabah. REUTERS/Hamad I Mohammed

Kasar Kuwaiti ta amince da baiwa Iraqi bashin dala biliyan daya tare da zuba hannun jarin wani kashin makudan kudin na dala biliyan guda, domin taimaka wajen sake gina kasar ta Iraqi.


Sarkin Kuwaiti Shiekh Sabah al-Jaber al-Sabah ne ya bada tabbacin a yau Laraba yayin da ake kammala taron kasashen duniya kan sake gina Iraqi da yaki ya rusa, taron da kasar ta Kuwaiti ta karbi bakunci.

An dai kiyasata cewa, sake aikin gina Iraqi zai lashe sama da dala biliyan 88. Zuwa yanzu kuma kungiyoyi masu zaman kansu zun yi alkawarin bayar da dala miliyan 330, baya ga taimakon na kasar Kuwaiti.

A baya-bayan nan ne dai kasar ta yi shekalar neman taimako don tallafa mata wajen farfadowa daga halin da ayyukan ta'addancin kungiyar IS ya jefa ta ciki.