rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Turai NATO/ OTAN

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Stoltenberg ya gargadi kasashen EU kan NATO

media
Sakataren kungiyar tsaro ta Jens Stoltenberg REUTERS/Eric Vidal

Sakataren kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg, ya gargadi kasashen Turai da su yi hattara, ka da sabon kawancen tsaron da suka kulla a tsakaninsu ya gurgunta ayyukan kungiyar ta NATO.


Jens Stoltenberg, ya bayyana wannan shakku ne a dai dai lokacin da ministocin tsaron kasashe mambobi a kungiyar ta NATO ke shirin gudanar da taro a birnin Brussels a wannan Laraba.

A cikin watan Disamban da ya gabatar ne kasashen na Turai suka sanar da kulla kawance domin karfafa tsaro a tsakaninsu, duk da cewa dukkaninsu mambobi ne a kungiyar ta NATO, lamarin da wasu ke ganin cewa zai iya haddasa matsala ga manyan manufofin kungiyar.

Amurka dai na daya daga cikin kasashen da ke sukar sabon kawacen tsaron na kasashen Turai, tare da kafa hujjar cewa hakan zai iya rage adadin kudaden da suke bai wa kungiyar NATO domin daukar dawainiyar NATO.

Duk da kokarin da kasashen na Turai ke yi domin jaddada NATO a matsayin wadda za ta ci gaba da tabbatar da tsaronsu, manazarta na ganin abin da kamar wuya tauna taura biyu a baki.