Dakarun Syria sun kashe mutane sama da 100 a Ghouta
Hare-haren bama-bamai da dakarun gwamnatin Syria suka kaddamar sun kashe sama da mutane 100 da suka hada da kananan yara 30 a yankin gabashin Ghouta da ke hannun ‘yan tawaye.
Wallafawa ranar:
Kungiyar da ke sanya ido kan Syria da tawagar agaji sun tabbatar da alkaluman mamatan da aka bayyana a matsayin mafi muni tun bayan da aka yi wa yankin kawanya a shekarar 2013.
Har ya zuwa safiyar wannan Talata, rundunar tsaren fararen hula a Syria ta ce, an ci gaba da kaddamar da hare-haren bama-baman, in da sama da mutane 40 suka mutu.
Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci kawo karshen hare-haren, in da ta ce sun wuce gona da iri.
A mnakon jiya ne yankin na Ghouta mai dauke da mutane kusan dubu 400 ya samu agajin farko a cikin watanni uku.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu