rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Syria Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres Faransa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Rasa rayukan fararen hula a Syria abin tada hankali ne - Guterres

media
Wani karamin yaro zaune a gaban wasu gine-gine da hare-haren jiragen yaki suka rusa a yankin Arbin da ke gaf da birnin Damaskas. REUTERS/Bassam Khabieh

Kasashen Duniya na ci gaba da matsin lamba ga gwamnatin Syria kan ta kawo karshen munanan hare-haren da ta ke kai wa kan fararen hula a yankin Ghouta wanda yanzu haka yayi sanadin hallaka fararen hula sama da 300.


Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya bayyana kashe-kashe a matsayin abin tada hankali wanda yayi kama da wutar Jahannama a doron kasa.

Shi kuwa shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya bukaci tsagaita wuta cikin gaggawa domin gudanar da ayyukan jinkai a yankin na gabashin Ghouta.

Yau ake saran kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai kada kuriā€™ar amincewa da tsagaita wutar kwanaki 30 domin kai kayan agaji ga mazauna yankin.

Rahotanni sun ce akasarin asibitocin yankin sun rushe sakamakon hare haren.