Isa ga babban shafi
Rasha

Rasha ta kera shu'umin makami gagara-gasa

Rasha ta samu nasarar kera katafaren makami mai linzami gagara-gasa da babu wani matakin kariya ko tsaro na zamani da zai iya kakkabo shi.Shugaba Vladmir Putin ya ce, makamin zai iya kai wa duk in da aka harba shi a duniya, komai nisan tazararsa.

Rasha ta ce, duk kasar da ta takale ta za ta dandana kudarta
Rasha ta ce, duk kasar da ta takale ta za ta dandana kudarta Ministry of Defence of the Russian Federation/Handout via REUTE
Talla

Shugaba Putin ya bayyana haka ne a yayin jawabin da ya gabatar na bayyana wasu daga cikin muhimman manufofin da gwamnatinsa za ta mayar da hankali, idan ya sake cin zaben shugabancin kasar karo na 4, wanda za a yi nan da kwanaki 17.

Putin wanda ya yi karin bayani kan karfin sabon makamin mai linzami ta hanyar nuna misalinsa  a hoton bidiyo, ya ce makaman kariya na zamani da Amurka ta girke a nahiyar Turai da Asiya, ba za su iya hana makamin isa duk in da yasa gaba ba.

Shugaban na Rasha ya kuma bayyana wasu makamai masu linzami na karkashin ruwa da kasar ta samu nasarar kerawa, wadanda ke da karfin keta dukkanin matakan tsaron zamani da aka dauka a matsayin kariya, baya ga layar zanar da suke da ita na fakewa.

Putin ya ce, babbar manufar mallakar karfin sojan Rasha shi ne tabbatar da zaman lafiya a Duniya, sai dai ya yi gargadin duk wata kasa da ta yi gangancin kai wa Rashan hari makaman nukuliya, za ta fuskanci martani nan take.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.