Isa ga babban shafi
Korea ta Arewa- Korea ta Kudu

Ina son karfafa zumunci da Korea ta Kudu- Kim Jong Un

Shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un ya ce, yana matukar son karfafa kusanci da Korea ta Kudu kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka rawaito.

Shugaba Kim Jong Un tare da manyan jami'an gwamnatin Korea ta Kudu
Shugaba Kim Jong Un tare da manyan jami'an gwamnatin Korea ta Kudu House/Yonhap via REUTERS
Talla

Wannan na zuwa ne bayan wasu manyan jami’an gwamnatin Korea ta Kudu sun kai wata ziyara ta musamman a birnin Pyongyang, in da kuma suka yi liyafar cin abincin dare tare da shugaba Kim duk da dabi’arsa ta kin shiga jama’a.

Jami’an dai su ne na farko daga bangaren gwamnatin Korea ta Kudu da suka gana da shugaba Kim tun bayan darewarsa kan karagar mulki.

Rahotanni na cewa, kasashen biyu sun cimma matsayar zama a teburin tattaunawa nan gaba don kara fahimtar juna kan takun sakan da ya shiga tsakaninsu.

Ana saran tawagar ta Korea ta Kudu ta kai ziyara Washington a cikin wannan makon don yi wa hukumomin Amurka karin haske kan abin da suka tattauna da Korea ta Arewa.

Amurka dai na takun saka da Korea ta Arewa saboda gwaje-gwajenta na makamamin nukiliya tare da yin barazanar mayar da Amurka toka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.