Isa ga babban shafi
Myanmar

Myanmar ta ci gaba da yi wa Muslmin Rohingya kisan-mummuke

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, kasar Myanmar na ci gaba da kokarin share al’ummar Musulmin Rohingya na jihar Rakhine daga doran kasa, in da ta ke yi musu kisan-mummuke.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, har yanzu ana cin zarafin Musulman Rohingya a Myanmar
Majalisar Dinkin Duniya ta ce, har yanzu ana cin zarafin Musulman Rohingya a Myanmar AFP
Talla

Wannan na zuwa ne bayan sojojin Myanmar sun murkushe Musulman Rohingya watanni shida da suka gabata, lamarin da ya tilsata wa mutane dubu 700 neman mafaka a Bangladeh.

'Yan kabilar Rohingya sun bayyana cin zarafin da suka fuskanta na kisa da fyade da kuma kona gidajensu daga sojojin Myanmar.

Mataimakin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya ta fannin kare hakkin bil’adama da ya gana da ‘yan kabilar Rohingya, Andreew Gilmour ya ce, babu shakka har yanzu an ci gaba da kokarin kawar da kabilar daga doran kasa.

Gilmour ya ce, yanzu haka ana yin matsin lamba ga Musulman Rohiinga da ke ci gaba da zama a Myanmar ta hanyar yi mu su ukuba da yunwa da kananan hare-hare don ganin sun kwashe komatsansu zuwa Bangladesh.

Jami'in ya ce, babu alamar da ke nuna cewa, nan gaba Musulman Rohingya za su koma Myanmar duk da alkawarin da gwamnatin kasar yi na fara mayar da su cikin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.