Isa ga babban shafi
Saudiya-Birtaniya

Ziyarar Yariman Saudiya na fuskantar bore a Ingila

Yarima Mohammed bin Salman na Saudiya ya fara ziyarar kwanaki uku a Birtaniya duk da zanga-zangar adawa da rawar da kasarsa ke takawa a yakin Yemen.

Yarima Mohammed bin Salma na Saudiya.
Yarima Mohammed bin Salma na Saudiya. REUTERS/Faisal Al Nasser
Talla

Salman mai shekaru 32 zai gana da firaministar Birtaniya, Theresa May kafin ya halartar lifayar cin abincin dare tare da sarauniyar Ingila.

Ana ganin tattaunawar  May da Yarima Salman za ta mayar da hankali ne kan tattalin arzikin Saudiya baya ga batun halin da al’umma ke ciki a Yemen.

Ana saran masu zanga-zanga su yi dandazo a kofar harabar gidan gwamnatin Birtaniya don nuna adawa da kisan fararen hula da Saudiya ke jagoranta a Yemen.

Ana kallo Yarima Salman a matsayin jagoran samar da sauye-sauye na zamani a Saudiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.