rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Afrika Amurka China Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Amurka ta gargadi Afrika kan hulda da China

media
Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson na ziyara a kasashen Afrika REUTERS/Jonathan Ernst

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson ya bukaci kasashen Afrika da su yi taka-tsan-tsan wajen rasa ‘yancinsu ta hanyar karbar basukan kudade daga China da ta kasance babbar abokiyar huldar kasuwancin nahiyar.


Mr. Tillerson na amfani da ziyar diflomasiyarsa ta farko a Afrika don karfafa huldar tsaro a nahiyar wadda ke ci gaba da karkata hankalinta ga China ta fuskar agaji da huldar kasuwanci.

Sai dai a cewar Tillerson ba wai fa yana kokarin dakile zuba hannayen jarin da China ke yi a Afrikan ba ne kamar yadda ya shaida wa manema labarai a birnin Addis Ababa na Habasha.

Tillerson ya ce, ya dace kasashen na Afrika su yi taka tsan-tsan da yarjeniyoyin da suke kullawa da China don kaucewa rasa yancinsu na mulkar nahiyarsu da kansu.

Kazalika Tillerson zai nemi inganta hulda da Afrika bayan shugaba Donald Trump ya bayyana ta a matsayin matattarar kazanta a cikin watan Janairun da ya gabata, lamarin da ya harzuka shugabannin nahiyar tare da mayar ma sa da martani duk da cewa, ya musanta furta kalaman.

Amurka dai ta kasance ja-gaba wajen bada taimako ga Afrika amma a shekarar 2009 ne, China ta yi ma ta fintinkau a matsayin aminiyar nahiyar ta fannin cinikayya.

China ta zuba hannayen jari na biliyoyin Dala don gudanar da aikin samar da kayayyakin more rayuwa a nahiyar, amma duk da haka ta na shan suka daga wasu masharhanta da ke cewa kasar na neman kane-kane a nahiyar.