Isa ga babban shafi
Korea ta Arewa- Amurka

Ana shirin ganawa tsakanin Kim Jong-un da Donald Trump

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un ya ce a shirye ya ke ya gana da takwaransa na Amurka Donald Trump nan zuwa watan mayun wannan shekara, tare da yin alkwarin cewa, zai dakatar da gwaje-gwajen makaman nukiliya da kasar ke yi.

shugaban Koriyar ta Arewa  Kim Jong-un tare da Chung Eui-yong, mai baiwa shugaban kasar Koriya ta Kudu shawara kan lamuran tsaro
shugaban Koriyar ta Arewa Kim Jong-un tare da Chung Eui-yong, mai baiwa shugaban kasar Koriya ta Kudu shawara kan lamuran tsaro The Presidential Blue House/Yonhap via REUTERS
Talla

Wannan dai, tabbaci ne da ke kunshe a wani sako da shugaban na Koriya ta Arewa ya aika wa takwaransa na Amurka ta hannun wasun manyan jami’an gwamnatin Koriya ta Kudu, kuma tuni shugaban na Amurka Donald Trump ya amice ya ganawa da takwaransa nasa Kim Jong-un.

Kamar yadda jami’an diflomasiyyar kasar Koriya ta Kudu suka bayyana a birnin Washington, shugaba Jong-un ya ce yana a shirye ya bayar da umurnin dakatar da duk wasu gwaje-gwajen makaman nukiliya da kasar ta share tsawon shekaru tana yi kafin wannan ganawar.

Chung Eui-yong, wanda ke jagorantar tawagar Koriya ta Kudu ne, ya mika wa shugaba Donald Trump goron gayyatar a jiya alhamis, bayan da wasu manzannin Seoul suka kai ziyara tare da ganawa da Kim Jong-un a farkon wannan mako.

Wannan dai na nuni da cewa, an samu gagarumin cigaba a kokarin kwantar da hankula tsakanin kasashen biyu, da suka mallaki makaman nukiliya, sannan kuma suka zafafa barazanar kai wa juna hari, musamman daga lokacin da Donald Trump ya dare kan karagar mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.