rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar Italiya Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Nijar ta jingine aniyar karbar sojin Italiya a kasar

media
Wasu daga cikin sojin Italiya a birnin Kabul na Afganistan mai fama da rikici Reuters/Ahmad Masood

Gwamnatin Jamhuriyar ta jingine aniyarta ta bai wa kasar Italiya damar jibge sojojinta a cikin kasar, bayan da Nijar ta amince da wannan mataki a cikin shekarar da ta gabata.


Da farko dai Jaridar Corriere della Sera da ake bugawa a kasar ta Italiya, ta ce sau biyu jere da juna, Ministan Tsaron Nijar, Kalla Moutari na rubuta wa takwararsa ta Italiya, Roberta Pinotti wasikar da ke rokon Italiya ta jibge sojojinta a Nijar amma Italiya ta ki, to sai dai Ministann Tsaron na Nijar ya musanta wannan ikirari.

A cikin watan Janairun da ya gabata ne, Italiya ta sanar da shirin aika dakarunta 470 domin taimaka wa a fagen yaki da ta’addanci da sarafarar mutane kamar dai yadda sauran kasashe irinsu Amurka, da Faransa da kuma Jamus suka yi.

Nijar na daya daga cikin kasashen yankin Sahel da ke fama da ayyukan ta'addanci da suka hada da rikicin Boko Haram duk da cewa, hare-haren kungiyar sun lafa a 'yan kwanakin nan a kasar.