Isa ga babban shafi
Syria

Fararen hula dubu 40 sun tsere daga Syria a rana guda

Majaliasar Dinkin Duniya ta yi gargadin yiwuwar ci gaba da ruruwar rikicin Syria duk da kada kuri'ar tsagaita wutar da zauren sulhunta ya yi a baya-bayan nan don samun zarafin shigar da kayakin agajin abinci da magunguna ga dubban fararen hular da ke yankin gabashin Ghouta da sauran sassan kasar.

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasar syria  ta ce a yau juma’a akalla fararen hula 41, da kananan yara 6 ne aka kashe a barin wuta ta sama a yankin kafra batna.
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasar syria ta ce a yau juma’a akalla fararen hula 41, da kananan yara 6 ne aka kashe a barin wuta ta sama a yankin kafra batna. REUTERS/Omar Sanadiki
Talla

Gargadin na Majalisar Dinkin Duniya na zuwa ne a dai dai lokacin da wasu bayananta ke nuna yadda adadin fararen hula fiye da dubu 40 suka tsere daga yankin na gabashin Ghouta a jiya alhamis kadai, matakin da ke nuna yadda rikicin ke kara tsananta tare da razana dubban fararen hular da ke yankin.

Babban jami'in Majalisar mai shiga tsakani kan rikicin na Syria Staffan de Mistura ya ce a baya duk da tsananin yakin da kasar ke fuskanta adadin mutanen da ke ficewa a Syrian baya wuce dubu 12 zuwa 20, amma adadin na mutane fiye da dubu 40 ya nuna yadda rikicin ke kara tsananta.

De Mistura ya ce kawo yanzu bangaren gwamnati da kawayenta na ci gaba da luguden wuta a yankin na gabashin Ghouta duk da cewa Majalisar Dinkin Duniya ta kada kuri'ar tsagaita wutar kwanaki 30.

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasar syria ta ce a yau juma’a akalla fararen hula 41, da kananan yara 6 aka kashe a wani luguden wuta ta sama da sojin Rasha suka kai yankin kafra batna na kasar ta Syria.

A cewar shalkwatan tsaron rasha, ko a yau Juma a akwai karin mutane dubu 2  da suka fice daga yankin na Gabashin Ghouta sakamakon luguden wutar da ake ci gaba da yi don fatattakar sauran 'yan tawayen da suka rage.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.