rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Korea ta Arewa Amurka Sweden Nukiliya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ministan wajen Korea ta Arewa ya isa Sweden kan ganawar Trump da Kim

media
Ministan harkokin wajen Korea ta arewa Ri Yong Ho bayan isarsa Sweden a wani bangare na sharar hanya kan tattaunawa tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da Kim Jung Un. © Mandatory credit Kyodo/via REUTERS

Ministan Harkokin wajen Koriya ta Arewa Ri Yong Ho ya gana da jami’n gwamnatin Sweden a wani yunkuri da ake tunanin cewar zai bude kofar tattaunawa tsakanin shugaban kasar Kim Jong Un da takwaran sa na Amurka Donald Trump.


Rahotanni sun ce Minista Ho ya gana da Firaminista Stefan Lofven da kuma ministan harkokin wajen sa Margot Wallstrom mako guda bayan shugaba Trump ya amince da shirin ganawa da shugaba Kim.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Sweden Pezhman Fivrin yace ganawar zata cigaba zuwa gobe asabar.

Kasar Sweden ke wakiltar kasashen Amurka da Canada da kuma Australia wajen huldar da ta shafi Koriya ta Arewa.