Isa ga babban shafi
Vietnam

Vietnam da Amurka na kulla alaka duk da kisan kiyashin 1968

Vietnam na bikin cika shekaru 50 da kafuwa tun bayan kisan kiyashin da Amurka ta yi wa dubban jama’ar kasar a kokarin da suka yi na ganin sun dakile Amurkan daga mamaye kasar.Bikin na yau wanda ke gudana a yankin My Lai mai dogon tarihi na samun halartar iyalan wadanda suka mutu yayin fafutukar kafa kasar dama sauran masu shiga tsakani kan yakin kasar ciki har da Amurkawa 60.

Firaministan Vietnam Nguyen Xuan Phuc yayinda ya ke gaisawa da takwaransa Firaministan Australia Malcolm Turnbull yayin bikin cikar kasar shekaru 50 da samun ‘yancin kai.
Firaministan Vietnam Nguyen Xuan Phuc yayinda ya ke gaisawa da takwaransa Firaministan Australia Malcolm Turnbull yayin bikin cikar kasar shekaru 50 da samun ‘yancin kai. AAP/Mick Tsikas/via REUTERS
Talla

A ranar 16 ga watan Maris din 1968 kadai Sojin Amurka sun hallaka al’ummar Vietnam fiye 504 a sansanin Son My yayin wata fafatawa a yunkurin da ta yi na kwace iko da wasu tsaunuka da ke yammacin My Lai.

A cewar Dang Ngoc Dung shugaban yankin Quang Ngai duk da abubuwan da suka faru tsakanin amurkawan da al’ummar kasar, Son My ta samar da wanzajjen zaman lafiya tare da yafewa Amurkawa har ma da basu damar shiga cikin kasar don ibada don su san gaskiya kuma su samu nutsuwar zuciya.

Wani daga cikin wadanda suka tsira da rayukansu yayin fafatawar ta 1968 yayin taron na yau, ya bayyana irin razani da suka shiga lokacin da suke binne ‘yan uwansu fiye da 500 saboda suna tunanin Amurka ka iya kawo wani harin da zai hallakasu baki daya.

Duk da kasancewar rikicin Vietnam da Amurka shi ne mafi munin laifukan yaki da Amurkan ta aikata a tarihi, amma a cewar shugabancin kasashen biyu yanzu lokaci ne da dangantaka ke kara kulluwa a tsakaninsu tare da yafewa junansu.

Bikin dai na zuwa ne adai dai lokacin da bai wuce mako guda ba da wakilcin Amurkan ya isa Vietnam duk dai a kokarin kara dankon zumunci tare da yafewa juna kan abin da ya faru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.