Isa ga babban shafi
Rasha

Vladmir Putin ya lashe wa'adi na hudu a matsayin shugaban kasar Rasha

Shugaban Rasha Viladimir Putin ya sake lashe zaben shugabancin kasar Rasha da aka gudanar a yau lahadi 18 ga watan maris din nan 2018.Sakamakon wata kuri’ar Jin ra’ayi da aka gudanar gabannin zaben ta nuna cewa, kusan kashi 70 na ‘yan kasar ta Rasha sun goyi bayan Putin.

Vladimir Poutine a wata rumfar zabe  à Mosco 18 maris 2018.
Vladimir Poutine a wata rumfar zabe à Mosco 18 maris 2018. Yuri Kadobnov/POOL via Reuters
Talla

Putin wanda ya ke kan shugabancin Rasha tun daga shekarar 2000, ya kara ne da abokan hamayya bakwai, daga cikinsu akwai attajirin kasar mai ra’ayin gurguzu Pavel Grudinin, Ksenia Sobchak wata tsohuwar ma’aikaciyar talabijin, sai kuma Vladmir Zhirinovsky wani sanannen mai ra’ayin kishin kasa.

Madugun ‘yan adawar kasar ta Rasha Alexei Navalny bai samu shiga zaben ba, sakamakon haramcin hakan da kotu ta yi masa bisa samunsa da laifin aikata almundahana, matakin da Navalny ya bayyana a matsayin makircin siyasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.