Isa ga babban shafi
Turkiya

Turkiya ta yi zazzafan martani kan rahoton MDD

Gwamnatin Turkiya ta caccaki rahoton Hukumar Kare Hakkin Bil’adama ta Majalisar Dinkin Duniya da ke nuna gagarumin keta hakkokin jama’a a kasar tun bayan dakile yunkurin juyin mulkin shekarar 2016.

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan na zargin malamin addinin kasar, Fethulla Gulen da ke zaune a Amurka da shirya yi ma sa juyin mulki a shekarar 2016
Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan na zargin malamin addinin kasar, Fethulla Gulen da ke zaune a Amurka da shirya yi ma sa juyin mulki a shekarar 2016 Yasin Bulbul/Presidential Palace/Handout via REUTERS
Talla

Rahoton ya ce, kimanin mutane dubu 160 aka tsare a karkashin dokar ta baci ta watanni 18 da gwamnatin Turkiya ta ayyana, in da kuma ta sallami ma’aikata dubu 152 da ake zargi da hannu a yunkurin juyin mulkin.

A yayin mayar da zazzafan martani, Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiya ta caccaki Kwamishinan Hukumar Kare Hakkin Bil’adama ta Majalisar Dinkin Duniya da ta ce, yana kokarin sauya tsarin tafiyar da hukumar don zama wata cibiyar hada kai da kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Ma’aiktar ta bayyana rahoton a matsayin mai kunshe da bayanan karya da kuma daukan bangaranci, abin da ta ce, Turkiya ba za ta amince da shi ba.

Tun dai a cikin watan Yulin shekarar 2016 ne, Turkiya ta kafa dokar ta baci bayan yunkurin kifar da gwamnatin kasar, yayin da a cikin watan Janairun bana ta tsawaita dokar a karo na shida.

Rahoton ya gargadi cewa, mahukunta na da karfin da ya wuce kima, abin da ke haddasa karan tsaye ga dokoki tare da tabarbarewar ‘yancin jama’a.

Kwamishinan Hukumar, Zeid Ra’ad Al Hussain ya ce, kusan mutane dubu 160 aka tsare, in da kimanin dubu 152 suka rasa ayyukansu a karkashin dokar ta bacin, bayan gwamnatin shugaba Recep Tayyip Erdogan ta zarge su da mara wa, malamin addinin kasar, Fethulla Gulen da ake zargi da shirya yujin mulkin duk da cewa yana zaune a Amurka.

Rahoton ya ce, mutanen da ke tsare na fuskantar azbatwarwa da kuma cin zarafi ta hanyar lalata da mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.