Isa ga babban shafi
Sauyin yanayi

An kashe fitilu a manyan biranen duniya saboda sauyin yanayi

Gidan Siniman Sydney da Hasumiyar Eiffel da ke Paris da Dandalin Red Square da ke Moscow na daga cikin wurare daban-daban a duniya da aka kashe fitilunsu da daddare a karshen mako domin janyo hankalin kasashen duniya kan illar da sauyin yanayi ke haifarwa.

Hasumiyar Eiffel da ke birnin Paris na cikin wuraren da aka kashe fitilunsu a saasan duniya
Hasumiyar Eiffel da ke birnin Paris na cikin wuraren da aka kashe fitilunsu a saasan duniya AFP/Geoffroy Van Der Hasselt
Talla

Shi dai wannan yunkurin da aka ma sa lakabi da ‘Earth Hour’ ya samo assali ne daga kasar Australia a shekarar 2007, kuma yanzu haka yana samun goyan baya a kasashe 187 na duniya, wadanda suka kashe fitilunsu da misalin karfe 8.30 na daren Asabar.

Dermot O’Gorman, mai jagorancin shirin a Australia ya ce, aniyarsu, ita ce janyo hankalin mutane kan muhimmancin kare muhalli da kuma dabbobi.

A Faransa in da aka kashe fitilar Eiffel Tower, shugaba Emmanuel Macron ya bukaci 'yan kasar da su hada kai wajen yaki da gurbata muhalli, in da yake cewa lokacin watsi da matsalar gurbacewar yanayi ta wuce.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guteres ya ce, shirin na zuwa a dai dai lokacin da ake samun karuwar matsalar sauyin yanayi da ke yin illa ga jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.