rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa Saudiya Yemen

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Faransawa na adawa da siyar wa Saudiya makamai

media
Shekaru uku kenan da Saudiya ta fara jagorancin hare-hare a Yemen REUTERS/Khaled Abdullah

Faransawa 3 daga cikin 4 ba sa kaunar ganin kasar ta sayar wa Saudiya makamai da sauran kayan aikin soji, kamar yadda wata kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna wadda aka gudanar albarkacin cika shekaru 3 da Saudiya ta jagoranci rundunar kasashen Larabawa 'yan sunni wajen kaddamar da yaki kan gwamnatin 'yan Houthi mabiya akidar Shi'a a Yemen.


Binciken da cibiyar YouGov ta gudanar ya nuna cewa kashi 74% na Faransawa na kyamar sayar wa Saudiya makaman yaki da kayayyakin aikin soja.

Kahi 71% na Faransawan kuma, ba sa kaunar sayar wa Daular Larabawa da sauran kasashen kawancen da ke goyon bayan dakarun gwamnatin Yemen wajen yakar 'yan tawayen Houthi da ke samun goyon bayansu daga kasar Iran, wajen ci gaba da rike birnin Sanaa babban birnin kasar ta Yemen.

Kimanin kashi 88% na Faransawan na fatan ganin Faransar ta dakatar da sayar da makaman ga kasashen da ake ganin za su iya amfani da su akan fararen hula.

Daga karshe kashi 69% na Faransawan da aka tambayi ra'ayinsu na goyon bayan kara karfafa matsayin Majalisar Dokokin Kasar ta Fransa a cikin duk wata harka da ta jibanci sayarwa wata kasa ta ketare da makamai.

Masu rajin kare hakkin jama'a sun bukaci shugaban Fransa Emmanuel Macron da ya gaggauta kawo karshen sayar da makaman kirar Faransa ga kasashen mulkiyar yankin Golf, da a halin yanzu ke ci gaba da yaki a kasar Yemen, ta hanyar karkata makaman da suka saya a kan fararen hula.