Isra'ila ta yi watsi da binciken kisan Falasdinawa a Gaza
Kasar Isra'ila taki amince wa da bukatar gudanar da bincike mai zaman kansa kan yadda sojojinta suka kashe Falasdinawa 16 da kuma jikkata daruruwa da ke zanga zangar lumana a kusa da iyakar Gaza da Isra'ila.
Wallafawa ranar:
Firaminista Benjamin Netanyahu ya yaba wa sojojinsa saboda rawar da suka taka, yayin da Ministan tsaro, Avigdor Liebermann ya ce babu wani bincike da za a gudanar.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres da Shugabar Diflomasiyar Kasashen Turai Federico Mogherini sun bukaci gudanar da bincike kan lamarin.
Shugaban Falasdinu Mahmud Abbas yayi Allah wadai da kisan, in da kuma ya bukaci samar da tsaro a yankinsu.
"A yau ina bukatar Majalisar Dinkin Duniya da ta gagagauta samar da tsaro a yankinmu na Falasdinu mai ‘yanci, lura da irin kiyayya da ake nuna mana. Ina dora wa hukumomin Isra'ila cikakken laifin kisan mutanen da suka yi shahada a yau ta hanyar wutar da dakarunsu na mamaya suka bude mu su a yayin fuskantarsu da zanga-zangar lumana game da yankinsu." In ji Abbas.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu