Isa ga babban shafi
Turkiya

Rasha da Turkiya sun kulla yarjejeniyar cinakin makaman tsaron sararin samaniya samfarin S400

SHUGABAN Rasha Vladimir Poutine ya bayyana cewa kasarsa zata gaggwata baiwa Turkiya makaman kariyar sararin samaniya samfarin S-400 da Turkiyar ta yi oda daga kasar.Wannan mataki na zuwa ne bayan da a jiya talata shugaban kasar turkiya Recep Tayyip Erdogan da takawaransa Rasha Vladimir Poutine, suka jagoranci kaddamar da gina cibiyar samar da makamashin wutar lantarki ta nukliya ta farko a kasar Turkiya, bayan da kasashen 2 suka fuskanci mummunar tabarbarewar diflomasiya a tsakaninsu a kasrshen 2015.

Vladimir Poutine da Recep Tayyip Erdogan à Ankara, 3 afrilu 2018.
Vladimir Poutine da Recep Tayyip Erdogan à Ankara, 3 afrilu 2018. Sputnik/Mikhail Klimentyev/Kremlin via REUTERS
Talla

Shuwagabanin kasashen 2 dake da ruwa da tsaki a cikin rikicin yakin kasar Syriya tare da kasar Iran dukkaninsu biyu na fuskantar tabarbarewar uldar diflomasiya da kasashen yammaci.

A lokacin wani taron manema labarai na hadin guiwa da shuwagabannin biyu suka jagoranta a Ankara, Shugaban Putin na Rasha ya sanar da takwaransa na turkiya Recep Tayyip Erdogan Putin ya bayyana cewa, bayan tattaunawa sun tsaida ruwan miya kan kwangilar, abinda ya rage kawai shine Rasha za ta yi iya kokarinta wajen ganin ta isar da wadannan na’urori karioya makamai masu linzame samfarin S400 a kan kari

A nasa bangaren M. Erdoganya kare matsayin kasarsa na son mallakar makaman kariyar sararin samaniyar, matakin da ke ci gaba da shan suka daga aminan kawancen turkiyar na kungiyar tsaro ta Nato ko Otan sakamakon banbancin da na’urorin tsaron keda su da na kasashen kawancen na turai

Inda ya kara da cewa mallakar makaman kariyar samaniyar samfarin S400 hurumin kasar Turkiya ne don haka sun riga sun tsada komai ya kammala a halin yanzu.

A watan satumbar bara shugaban na Turkiya M. Erdogan ya bayyana cewa Moscou da Ankara sun saka hannu kan wannan kwangila a yayinda wani mashawarci ga Putin ya bayyana kamalata yarjejeniya a watan December da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.