Isa ga babban shafi
Syria

Iran da Turkiya da Rasha sun hada kai kan Syria

Shugabannin kasashen Iran da Turkiya da Rasha sun lashi takobin aiki tare don samar da tsagaita wuta mai dorewa bayan cika shekaru 7 da barkewar yakin basasa a Syria. Shugabannin sun bayyana haka ne jim kadan da kammala wani taro da suka gudanar a birnin Ankara, in da suka tattauna game da zaman lafiyar Syria.

Shugaba Hassan Rouhani na Iran da Recep Erdogan na Turkiya da kuma Vladimir Putin na Rasha
Shugaba Hassan Rouhani na Iran da Recep Erdogan na Turkiya da kuma Vladimir Putin na Rasha Reuters
Talla

Shugaban Turkiya, Recep Tayyip Erdogan da takwarorinsa na Iran da Rasha wato Hassan Rouhani da Vladimir Putin sun jaddada yunkurinsu na hada kai don samar da tsagaita musayar wuta mai dorewa tsakanin bangarorin da ke yaki da juna a Syria.

Taron da shugabannin suka gudanar a birnin Ankara, shi ne irinsa na biyu bayan makwamancinsa da Putin ya karbi bakwanci a birnin Sochi a cikin watan Nuwamba, abin da ke nuna ci gaban da ake samu na hadin kai tsakaninsu.

Duk da cewa, babu wata takamammiyar matsaya da suka cimma jim kadan da kammala taron, amma shugabannin uku sun nuna alamar daukar mataki mai tsauri da masharhanta ke ganin ka iya dorewa.

Putin da Rouhani da Erdogan, dukkaninsu sun goyi bayan tattaunawar zaman lafiyar Syria a birnin Astana baya ga wadda Majalisar Dinkin Duniya ta jagoranta a birnin Geneva.

Sai dai shugabannin sun bayyana tsarin da suka dauka a ganawarsu ta Astana a matsayin wanda ya yi tasiri wajen rage tashe-tashen hankula a sassan Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.