Isa ga babban shafi
Brazil

Tsohon shugaban Brazil zai shafe shekaru 12 a gidan yari

Kotun kolin kasar Brazil ta ki amincewa da bukatar tsohon shugaban kasar, Inacio Lula Da Silva na jinkirta tasa keyarsa zuwa gidan yari bayan yi ma sa daurin shekaru 12 saboda samun sa da laifin cin hanci da rashawa.

Tsohon shugaban kasar Brazil, Inacio Lula Da Silva
Tsohon shugaban kasar Brazil, Inacio Lula Da Silva REUTERS/Leonardo Benassatto
Talla

Alkalan kotun 6 suka amince da tsohon shugaban ya kama hanyar gidan yari duk da daukaka kara kan hukuncin da ya yi, yayin da 5 suka ki.

A karon farko dai kawunan alkalan ya rabu, in da guda 5 suka goyi bayan tura tsohon shugaban gidan yari, yayin da 5 kuma suka ki, abin da ya bai wa shugaban alkalan kada kuri’arsa ta 6 wadda ta amince da tasa keyar sa zuwa gidan yarin.

A baya wata kotu ta samu tsohon Shugaba Lula mai shekaru 72 da laifin cin hanci da rashawa wajen karbar wani gida da ke bakin teku daga wani kamfanin gine-gine Odebretch a matsayin cin hanci, domin samun kwangiloli daga gwamnati, abin da ya sa Kotu ta daure shi shekaru 12 da wata aguda a gidan yari.

Kafin yanke hukuncin, shugaban sojin kasar, Janar Eduardo Villas Boas, ya fito fili ya bayyana goyan bayan tura Lula gidan yari, yayin da magoya bayansa ke danganta shari’ar da siyasa.

Lula na daga cikin 'yan takara na gaba-gaba da ke shirin fafatawa a zaben shugaban kasar da za ayi a ranar 7 ga watan Oktoba mai zuwa, sai dai wannan hukunci na iya dakile fatansa na komawa karagar mulki bayan shekaru 10 da ya yi a baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.