rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Daular Larabawa Lebanon

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kasar Daular Larabawa Za Ta Baiwa Sojan Lebanon Taimakon $200 miliyan

media
Shugabannin kungiyar Kasashen Larabawa rfi

Kasar Daular Larabawa ta yi alkawarin baira kasar Lebanon agajin kudaden da suka kai Dalan Amurka miliyan 200 don a farfado da Sojan Lebanon da za su iya kare kasar su.


Maaikatar Waje ta Daular Larabawa ta sanar cewa Dala Miliyan 100 za’a mika su ga Sojan Lebanon, sannan Dala Miliyan 100 a mika su ga sauran jamian tsaron Lebanon mai makwabtaka da kasar Syria wadda yaki ya tagayyara.

A wani taro da aka yi tsakiyar watan jiya a Rome kasashen duniya sun yi alkawarin tallafawa don farfado da sojan Lebanon.

Faransa kanta ta sanar da cewa za ta bada kudade bashi da suka kai Dalan Amurka miliyan 400.