Isa ga babban shafi
Syria

Harin makami mai linzami ya kashe sojin Syria

Wani makami mai linzami ya fada kan barikin sojin kasar Syria tare da kashe dakarun kasar da dama a cikin daren jiya, sa-o’i kadan bayan da Amurka da Faransa suka yi gargadin cewa za a dauki zazzafan mataki a kan kasar, biyo bayan zargin kai hari da makami mai guba da ake yi wa dakarun shugaba Bashar al-Assad a garin Douma da ake kallo a matsayin tungar ‘yan tawaye. 

Mutane da dama sun mutu a harin da aka kai wa dakarun sojin Syria a sansaninsu
Mutane da dama sun mutu a harin da aka kai wa dakarun sojin Syria a sansaninsu EUTERS/Khalil Ashawi
Talla

Zargin yin amfani da makami mai gubar da ake yi wa gwamnatin Assad dai ya haifar da tada jijiyoyin wuya daga shugabannin kasashe da dama, a yayin da aka ruwaito kafar watsa labarai ta cikin gida a kasar ta Syria na cewar, yanzu haka 'yan tawaye a yankin gabashin Gouta sun amince su kwashe kayansu daga yankin.

Sakataren Majalisar Dunkin Duniya Antonio Guterres, ya bayyana a fili cewar ya kadu da jin labarin yadda aka ce dakarun gwamnatin Assad tare da taimakon Sojin Iran da Rasha na ta antaya wa fararen hula makamai masu guba yana mai cewar wannan abin damuwa ne matuka.

A jiya Lahadi ma Fafaroma Francis ya bi sahun kasashen Amurka da Birtaniya wajen yin Allah-wadai da yadda ake harhada makami mai gubar tare da sakarwa al’ummar da ba su ji ba basu gani ba, a daidai lokacin da ake zargin cewar Sojin gwamnatin Syriar sun kai wa 'yan kasar hari da makami mai gubar da ya kashe akalla fararen hula dubu 1da 600 a lokaci guda.

Shugaban  Amurka Donald Trump ya ce hakika masu kai wannan harin za su yaba wa aya zakinta.

Shi ma shugaban Turkiyya Recep Teyyep Erdogan ya ce, hakika zargin da ake yi wa gwamnatin shugaba Assad abin damuwa ne matuka.

Idan ana iya tunawa dai Turkiyya ta kasance a baya, aminiyar kud-da-kud ga Syria, kuma daya daga cikin masu taimaka wa Assad yakar 'yan tawaye tare da Iran da kuma kasar Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.