rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Libya Majalisar Dinkin Duniya Rikicin Kasar Libya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Dubban mutane na tsare a hannun 'yan tawayen Libya

media
Dubban mutane na tsare a hannun kungiyoyi masu dauke da makamai a Libya REUTERS/Ismail Zitouny

Wani sabon rahoto na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa, akwai wasu dubban mutane maza da mata da ba a taba jin labarinsu ba da ke ci gaba da kasancewa cikin mawuyacin hali a hannun kungiyoyin ‘yan tawaye masu dauke da makamai a Libya


Rahoton wanda Hukumar Kare Hakkin Jama’a na Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a wannan Talata, ya bayyana cewa, ‘yan tawayen na azabtar tare da cin zarafin wadannan bayin Allah da ke tsare a hannunsu.

Shugaban Hukumar Kare Hakkin Jama’ar, Zeid Ra’ad Al Hussein ya ce, dole ne a kawo karshen keta hakkokin jama’a da cin zarafinsu a Libya, sannan kuma a hukunta wadanda aka samu da laifi.

Tun dai a shekarar 2011 ne Libya ta tsindima cikin tashin hankali bayan kifar da gwamnatin marigayi Moammar Gaddafi, lamarin da ya bai wa kungiyoyin ‘yan tawaye damar cin karensu babu babbaka.