rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa Saudiya Iran Yemen

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Saudiya da Faransa za su hana Iran sakat a gabas ta tsakiya

media
Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da Yariman Saudiya, Mohammed Bin Salman Saudi Press Agency/Handout

Kasashen Saudiya da Faransa sun amince da daukar matakin hana Iran fadada karfin ikonta a yankin gabas ta tsakiya, tare da bayyana shirin gudanar da tarukan bunkasa samar da kayan agaji ga Yemen, in da dakarun Saudiya ke yin luguden wuta.


A wannan ziyarar ta kwanaki uku da Yariman Saudiya, Muhammad Bin Salma ya kai a yankin kassahen yammacin duniya, shugaban kasar Faransa Emannuel Macron ya bukaci a kara matsa kaimi ga kokarin hanawa Iran kara samun gindin zama a yankin na gabas ta tsakiya.

A wannan kirkirarriyar dabarar da shugabannin kasashen suka fito da ita a tattaunawar tasu dai, akwai batun rage kaifin abinda suka kira musuluntattar Dimokradiyyar da a ganinsu kan iya kara kaifin ayyukan 'yan ta’adda a duk fadin yankin na gabas ta tsakiya.

Shugaban kasar ta Faransa wanda kuma ya bayyana Iran a matsayin makiyyiyar daukacin kasashen na Larabawa, ya kuma bukaci Saudi Arebiya da ta mutunta dokar kasa da kasa, ta hanyar dakatar da kai hare-haren da take a kasar Yemen inda Saudiyyar ke jagorancin Dakarun kasashen Duniya wajen kai wa 'yan tawayen Hutsi hare-hare, da kuma datse masu alaka da kowa tun a shekarar 2015 da ta gabata, abinda ya haddasa tsananin yunwa da barkewar cututtuka masu hallaka rayuka.

A ziyarar ta Yariman Saudi Arebiya dai shugabannin sun rattaba hannu ga yarjejeniyar musayar al’adu tare da kakkafa wuraren shakatawa a kasar ta Saudi Arebiya wadda ta kai kudi Dollar Amurka Billiyan 14 da doriya.

Dama dai Faransa ta gabatarwa Saudi Arebiya tayin bukatar taimakawa don gina gidajen Caca da sauran harkokin barje gumi da a baya ba’a yi a kasar ta Saudiyya.