rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Saudiya Tseren Keke

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An gudanar da gasar tseren keke ta mata karon farko a Saudiya

media
Wannan ne karon farko da aka gudanar da gasar tseren keken na mata a Saudiyya. Fabien Jannic-Cherbonnel/RFI

A Karon farko kasar Saudi Arabia ta gudanar da gasar tseren keke na mata, a karkahsin sauye sauyen da Yariman kasar, Muhammad ibn Salman ke aiwatar wa.


Rahotanni sun ce an gudanar da tseren kekunan ne a birnin Jeddah da ke kasar ta Saudi Arabia, inda mata 47 suka shiga gasar ta kilomita 10.

Wadda ta shirya gasar Nadima Abu al-Enein ta ce ta yi mamakin ganin yawan matan da suka shiga gasar, wanda a shekarun baya abu ne mai wuya a fadin kasar.

Nadima ta ce da an shirya mata 30 za su shiga gasar, amma kuma ganin yawan matan da suka fito ya sa suka kara zuwa 47.

Kasar Saudi Arabia na ci gaba da ganin sauye sauye tun bayan kama mulkin Sarki Salman bin Abdulaziz, wanda ya nada dan sa Muhammad a matsayin Yarima mai jiran gado.