rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Isra'ila Falasdinawa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An sake karawa yau Jumu'a tsakanin Sojin Israela da Falasdinawa

media
Des manifestants palestiniens brûlent un drapeau Israélien pendant le troisième vendredi de la «Grande Marche du retour» à la frontière entre Gaza et Israël, le 13 avril 2018. REUTERS/Ibraheem Abu Mustafa

Rahotanni daga kan iyakar zirin Gaza da Isra'ila na cewa an sami barkewar tarzoma yau Juma’a karo na uku kenan a jere, inda dubban masu zanga-zanga suka gwabza fada da Sojin Isra'ila wanda ya zuwa yanzu ya yi sanadiyar mutuwar Palestinawa 33 da jikkata daruruwansu.


A wurare daban daban ne dai aka bada labarin cewar Falasdinawan da ke jifa da duwatsu, a yayinda sojin Israela ke harbi da bindiga da hayaki mai sa kwalla, da kuma hayakin tayoyi da ke tashi ya turnuke ko'ina.

Falasdinawan akalla 30 ne suka jikkata a yau dinnan, baya ga mutum daya da ya mutu, sai kuma wasu ma'aikatan lafiya akalla 10 da suke shiga cikin wani hali saboda shakar gurbataccen Iska.

A cewar sojin Israela, sun dauki matakin da suka dauka ne saboda an yi kokarin lalata shingen da suka sa, kuma wai an kai harin ne da abubuwa masu tarwatsewa.

A wasu yankunan Gaza ma an kona tutocin Israela masu tarin yawa, tare da kona hoton Firaiministan Israela Benjamin Netanyahu da na Yarima mai jiran gado na kasar Saudiyya Mohammed Bin Salman wanda ake zargi da hada kai da Israela.

Dazun nan ne dai a wani taron Kwamitin Sulhu na MDD babban sakataren Majalisar Antonio Gutteres ya tabo batun Israela da Palestinawa.

Yau dai Juma'a ta 3 kenan sojin Israela na barin wuta kan Falasdinawan da ke boren tunawa da ranar 30 ga watan jiya. Kuma duk da sukar yadda Israela ke maida martani ta kafi da ake yi wa kasar, hakan take ganin ya fiye mata.