Isa ga babban shafi
Mali

An kashe mayakan da suka kai hari kan sojin MDD a Mali

Rundunar Sojin Faransa ta tabbatar da mutuwar wasu mayakan ‘yan tawaye 15 da suka kai farmaki kan sansanin dakarun Majalisar Dinkin Duniya da ke tsohon birnin Timbuktu a yankin arewacin Mali a karshen mako.

Wasu daga cikin dakarun kiyaye zaman lafiya a Mali
Wasu daga cikin dakarun kiyaye zaman lafiya a Mali Marie-Lan Nguyen / Wikimedia Commons
Talla

Rundunar Majalisar Dinkin Duniya da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Mali ta ce, an kashe daya daga cikin jami’anta a dauki ba dadin da aka yi amfani da makaman roka da manyan bindigogi da kuma wata mota makare da bama-bamai a sansanin rundunar da ke makwabtaka da filin jiragen sama na birnin Timbuktu, in da kuma wasu gommai suka jikkata.

Rundunar Sojin Faransa ta ce, bakwai daga cikin jami’anta ne kawai suka jikkata a harin, alkaluman da suka saba da wadanda hukumomin Mali suka bayar a farko, in da suka ce, jami’an Faransan 12 ne suka samu rauni.

Bayannai na cewa, maharan sun yi shigar burtu don sajewa da dakarun na wanzan da zaman lafiya da zimmar haddasa rudani a tsakanin sojojin da ke kokarin dakile harin.

Shugaban rundunar wanzan da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, Jean Pierre Lacroix, ya yi Allah-wadai da harin a shafinsa na Twitter , yayin da ya lashi takobin ci gaba da samar da zaman lafiya a Mali duk da wannan farmakin da aka kai a ranar Asabar da ta gabata.

Mai magaba da yawun rundunar siojin Faransa, Patrik Steiger ya ce, maharan sun gaza cimma muradunbsu na yin mummunar barna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.