rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Birtaniya Najeriya Muhammadu Buhari Theresa May

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Muhammadu Buhari ya gana da Theresa May

media
Firaministar Birtaniya Theresa May tare da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a birnin Landan REUTERS

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi wata ganawa ta musamman da Firaministar Birtaniya Theresa May yau Litinin. Ganawar na zuwa a dai dai lokacin da shugabannin kasashe renon Ingila ke wani taro a birnin na London.


Tattaunawar dai tsakanin bangarorin biyu ta shafi alakar da ke tsakanin Birtaniyar da Najeriya kamar yadda mataimakin shugaban na musamman kan kafofin sada zumunta Bashir Ahmad ya wallafa a Shafinsa na Twitter.

Muhammadu Buhari yayin ganawar ya kuma yabawa Teresa May kan kokarin da Birtaniya ke yi na horar da jami'an soji don kammala fatattakar kungiyar ta'addanci ta Boko Haram.

Shugabannin biyu ana saran za kuma su kara yin wata kebantacciyar ganawa ta musamman a taron kasashe renon Ingila da zai gudana a birnin na London.