rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Najeriya Donald Trump Muhammadu Buhari Ta'addanci Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Trump na Amurka ya gayyaci Buhari don ganawa da shi

media
Shugaban Amurka Donald Trump na gaisawa da shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya Premium Times

Fadar gwamnatin Amurka ta ce, shugaban kasar Donald Trump zai karbi bakwanci takwaransa na Najeriya, Muhammadu Buhari a ranar 30 ga wannan wata na Afrilu don tattaunawa kan batutuwan da suka shafi Najeriya, ciki har da matsalar ta'addanci da tattalin arziki.


A cikin wata sanarwa da ta fitar a yammacin jiya Lahadi, Fadar White House ta ce, shugaba Buhari zai gana da Trump a birnin Washington don tattaunawa kan fada da ayyukan ta’addanci da samar da tsaro da zaman lafiya da kuma habbaka tattalin arziki.

Kazalika tattaunawar za ta mayar da hankali kan gina Najeriya dangane da rawar da take takawa a matsayinta na jagorar demokradiya a yankin Afrika.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya rawaito cewa, Buhari, shi ne shugaba na farko daga Afrika da Trump ya kira kai tsaye ta wayar tarho jim kadan da rantsar da shi kan karagar mulkin Amurka a cikin watan Janairun bara.

Wannan ne ya sa masana siyasa ke ganin cewa, kiran da Trump ya yi wa Buhari ya nuna irin muhimmancin da Najeriya ke da shi a Afrika.