rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Turkiya Amurka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Turkiya ta gurfanar da wani ba'amurke gaban kotu kan ta'addanci

media
Shugaba Recep Tayyib Erdogan dai na zargin duk wani mai alaka da Fethullah Gulen a matsayin dan ta'adda, yayinda ya ke zargin Gulen din da hannu a yunkurin juyin mulkin kasar na 2016 da bai yi nasara ba. REUTERS/Umit Bektas/File Photo

Gwamnatin Turkiyya ta gurfanar da wani ba’amurke limanin Coci mazaunin kasar Andrew Brunson gaban kotu kan zargin taimakawa ayyukan ta’addanci baya ga alaka da fitaccen malamin addinin nan Fethullah Gulen.


Tun a watan Oktoban 2016 gwamnatin shugaba Recep Tayyib Erdogan ta kame Mr Brunson wanda shi ne shugaban wata Coci da ke birnin Izmir bayan da ta zarge shi da alaka da Fethullah Gulen.

Matakin kame Mr Brunson dai ya haddasa tsamin alaka tsakanin Turkiyyan da Amurka.

Turkiyya ta ce Mr Brunson yana taimakawa wata kungiyar ta’addanci karkashin jagorancin fitaccen malamin addinin nan Fethullah Gulen da ke gudun hijira a Amurka, bayan da Erdogan ya zargi cewa yana da hannu a yunkurin juyin mulkin kasar da bai yi nasara ba a 2016.

Mr Brunson mai shekaru 50 a duniya, matukar dai aka same shi da zargin da Turkiyyan ke yi akansa zai shafe akalla shekaru 35 a gidan yari.

Tun bayan kame Mr Brunson a wancan lokaci sai a yau ne Turkiyyan ta gurfanar da shi gaban Kotu a birnin Aliaga tare da jakadan Amurka kan al’amuran da suka shafi addini Sam Brownback da kuma Sanata Thom Tillis.

Tuni dai Mr Brunson ya musanta dukkanin zargin da Turkiyyan ke yi kansa, yayinda a bangare guda lauyan da ke kare shi, Cem Halavurt ya ce babu wasu kwararan hujjoji da ke tabbatar da zargin na Turkiyya, haka zalika bayanan da ta ke dasu baza su gamsar da kotu ba.