rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Renon Ingila Birtaniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kasashe renon Ingila na shirin zaben sabon shugaba

media
Sarauniya Elizabeth ta Ingila ta shafe tsawon shekaru tana jagorancin kungiyar kasashe renon Ingila tun bayan mutuwar mahaifinta, sarki George a shekarar 1952 REUTERS/Hannah McKay

Shugabannin Kasashe Renon Ingila na shirin zaben sabon jagoran kungiyar a taronsu da zai gudana a cikin wannan makon, kamar yadda fadar Firaministan Birtaniya ta sanar.


Sabon jagoran da ake sa ran sanarwa zai maye gurbin Sarauniya Elizabeth ta Ingila mai shekaru 91 wadda take a matsayin jagorar kasashen tun bayan mutuwar mahaifinta Sarki Geoge na 6 a shekara ta 1952, duk da cewa, ba gadon kujerar ake yi ba.

Kakakin fadar Firaministar Birtaniya ya bayyana cewa, a wajen taron da ke tafe a ranar Alhamis da Juma’a ne za a san wanda zai jagoranci kungiyar kasashen renon Ingila.

Babbar Sakatariyar Kungiyar Patricia Scotland, ta shaida wa manema labarai cewa, taron zai bai wa shugabannin damar magana da juna sosai.

Babu dai wasu bayanai da ke nuna cewa, ko 'ya'yan ita sarauniyar ne za su hau kujerar jagorancin kungiyar ta Commonwealth.

Sai dai kuma, babban danta, Yarima Charles  mai shekaru 69 ya wakilce ta a taron a shekara ta 2013 a Colombo, kafin sarauniyar ta rage yawan zirga-zirga.