rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Amurka BOKO HARAM

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Amurka ta bukaci Najeriya ta sauya dabarun yakar Boko Haram

media
A baya-bayan nan dai Amurkan na nuna damuwa matuka kan ayyukan ta'addancin da ke faruwa a Nahiyar Afrika. REUTERS/Kevin Lamarque

Amurka ta bukaci Najeriya ta sauya dabarun da ta ke amfani da su a yanzu wajen yakar Boko Haram la'akari da yadda mayakan ke kokarin bijirewa dabarun da ake amfani da su musamman kan yadda su ke ci gaba da hallaka daruruwan jama'a a hare-haren sari ka noken da su ke kai wa.


Yayin taron hafsoshin kasan kasashen Afrika da ke ci gaba da gudana a Abuja babban birnin Najeriyar wani babban hafson sojin Amurka da ke jagorantar taron Laftal kanal Sean McClure ya ce kamata ya yi a samar da sabbin dabaru matukar ana bukatar gaggauta fattattakar mayakan na Boko Haram.

Amurka dai na neman yin uwa da makarbiya ne waje ganin ta taimakawa kasashen Afrika da gabas ta tsakiya kammala yakar ayyukan ta'addanci kamar yadda Kanal McClure ya shaidawa manema labarai yayin wata ganawa ta musamman a taron can a Abuja.

Kanal McClure ya ce ayyukan ta'addanci a kassahen Afrika da suka kunshi na boko Haram a Najeriya Nijar, Kamaru da Chadi da kuma na Al-Qaeda a Mali ka iya zama tarihi matukar aka hada hannu.

A baya-bayan nan dai Amurkan na nuna damuwa matuka kan ayyukan ta'addancin da ke faruwa a Nahiyar Afrika, inda ta kaddamar da wani atisayen soji a Jamhuriyar Nijar daga kasashe 26 da suka kunshi 12 na Afrika da kuma 14 daga sauran sassan duniya da nufin yakar ayyukan ta'addanci a yankin Sahel.