Isa ga babban shafi
Syria

Syria ta kai farmaki Ghouta karon farko bayan zarginta da kai harin guba

Dakarun gwamnatin Syria sun kai hari da jiragen sama kan yankin Ghouta da ke gabashin birnin Damascus, karo na farko daga lokacin da aka fara zargin gwamnati da yin amfani da makami mai guba a garin Douma.

Wasu 'yan Syria kenan ke daga tutocin kasashen Iran Turkiyya da kuma Syria don nuna adawa da hare-haren kasashen yammaci a cikin kasarsu.
Wasu 'yan Syria kenan ke daga tutocin kasashen Iran Turkiyya da kuma Syria don nuna adawa da hare-haren kasashen yammaci a cikin kasarsu. REUTERS/Omar Sanadiki
Talla

Kungiyar da ke sanya ido kan lamurran da ke faruwa a rikicin kasar ta Syria, ta ce an jikkata mutane da dama a harin.

A jiya ne dai Jami'an da ke bincike kan amfani da makami mai gubar kan fararen hula suka isa birnin na Douma ko da yake dai shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce Rasha ta goge duk wasu hujjoji da ake da su na kai farmaki da makaman masu guba kan fararen hula, batun da Rashan ke ci gaba da musantawa.

Kasashen yammacin duniya dai da suka kunshi Birtaniya Faransa da kuma Amurka sun kai wasu farmaki Syrian kan abin da suka kira kunnen kashi da Bashar al-assad ya yi na kai hari da makami mai guba kan fararen hula.

Masharhanta dai na gani abu ne mai wuya Shugaba Assad ya kai farmakin da makami mai guba la'akari da cewa ya yi nasarar kwace kashi 90 cikin dari na yankunan da ke hannun 'yan tawaye da sauran 'yan bindiga, kuma ko a wancan lokaci bai yi amfani da makamancin makamin ba.

A jiyan ne dai kasashen Turkiyya da Iran suka kara jaddada matsayarsu na ci gaba da mara baya ga Syrian musamman kan hare-haren da kasashen na yammacin duniya suka kai mata.

A bangare guda suma kasashen Birtaniya da Faransa yanzu haka na ci gaba da shan suka daga al'ummarsu ganin yadda suka yi gaban kansu don kai harin Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.