Isa ga babban shafi
Iraqi

Har yanzu Kuwaiti na karbar kudaden ramako daga Iraq

Sama da shekaru 20 da rasuwar marigayi shugaban kasar Iraqi Saddam Husaini tun bayan mamayar da Iraqi ta yi wa kasar Kuwaiti a shekarar 1990, har yanzu kasar Kuwaiti na karbar kudaden ramako [diyya] daga kasar Iraqi. Na baya bayan nan shi ne na amincewa da biyan Dolar Amurka miliyan 90 da aka yi tsakanin kasashen a yau Jumu’a.

Hoton aikin zabe a kasar Kuwaiti
Hoton aikin zabe a kasar Kuwaiti REUTERS/Stringer
Talla

Biyan kudin dai shi ne na farko da Hukumar kula da biyan Diyyar ramako ta Majalisar dinkin Duniya ta amincewa tun shekarar 2014 lokacin da aka dan samu tawaya saboda matsalar tsaro da aka fuskanta a Iraqi.

Hukumar tsaro ta Majalisar dinkin Duniya ce ta kafa kwamitin biyan kudaden diyyar a shekarar 1991, shekara daya da Dakarun hadin Guiwa na Majalisar dinkin Duniya suka tilastawa Dakarun Saddam Husaini ficewa daga kasar Kuwaiti.

An dai amince a hukumance a biya Dolar Amurka biliyan 54 da miliyan 4 ga daidaikun mutane, da kamfunna kazalika da hukumomin gwamnati da kuma kungoyoyi masu zaman kansu da suka yi hasarar nan-take daga harin mamayar da dakarun kasar Iraqi suka kai wa Kuwaiti a wannan lokaci.

Ana kuma tatsar kudaden ne daga kudaden haraji da kuma na albarkatun Man Fetir daga kasar Iraqi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.