Isa ga babban shafi
Gaza

An kashe Falasdinawa 2 a zanga-zangar yau Jumu’a a Gaza

Rahotanni daga Gaza na cewa dakarun Isra’ila sun kashe akalla Fasladinawa biyu a zanga-zangar da falasdinawan suka gudanar a wannan juma’a. Yau dai makonni 4 kenan da mazauna yankin na Gaza ke gudanar da tarzoma domin nuna rashin amincewa da mamayar da Isra’ila ke yi wa al’ummar Palasdinu.

Yankin zirin Gaza
Yankin zirin Gaza REUTERS/Amir Cohen
Talla

Mutanen biyu da aka kashe a wannan juma’a matasa ne, daya mai shekaru 24, yayin da daya ke da shekaru 25 a duniya, kuma a cewar majiyar kiwon lafiya a yankin na Gaza, dukkaninsu an harke su ne da bindiga.

Sakamakon yadda dakarun na Isra’ila ke buda wuta akan duk wanda ya kusanci shingen da ya raba Gaza da Isra’ila, karo na farko dai Falesdinawan sun yin amfani da kwalabe da kuma balanbalan da aka cinnawa wuta domin jefa wa dakarun na Isra’ila.

Wannan dai sabon salo ne da masu tarzomar suka bullo da shi domin kalubalantar dakarun na Isra’ila wadanda ke cigaba da killace yankin na Gaza mai mutane kusan milyan biyu.

A tsawon makonni hudu da fara wannan zanga-zangar, jami’an tsaron na Isra’ila sun bindige Falesdinawa akalla 37.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.