rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa Amurka Nukiliya Iran Korea ta Arewa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Babu zabi na biyu kan yarjejeniyar nukiliyar Iran-Macron

media
Shugaban Faransa Emmanuel Macron da takwaransa na Amurka Donald Trump LUDOVIC MARIN / AFP

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da ke fara rangadin kwanaki uku a Amurka, ya bayyana aniyarsa ta shawo kan shugaba Donald Trump don ganin ya amince da yarjejeniyar nukiliyar Iran. A yayin ganawa da kafar Fox News, shugaba Macron ya ce, babu wani zabi da ya rage matukar aka soke wannan yarjejeniya.


Kalaman Macron na zuwa ne a dai dai lokacin da Trump ke ke nuna adawa da yarjejeniyar wadda a baya  ya sha bayyana ta a matsayin shirme.

"A game da nukiliya, me ka ke da shi a matsayin mafificin zabi, ni dai ban gani ba, bani da wani zabi na biyu game da nukiliyar Iran. Wannan ita ce ayar tammbayar da za mu tattauna akan ta" In ji Macron.

Macron ya ce,  "ya kamata a kaddamar da wannan tsarin  domin kuwa ya fi kyau fiye da halin da ake ciki kan sha’anin Korea ta Arewa."

Shugaba Trump dai na barazanar kekketa wannan yarjejeniyar da Iran ta cimma da manyan kasashen duniya a shekarar 2015 da zimmar takaita yunkurin mahukuntan Tehran kan mallakan nukiliya, abin da yasa aka sassauta ma ta tarin takunkuman da ke kanta.

Shugaba Trump na da nan da ranar 12 ga watan Mayu mai zuwa don yanke shawara kan ko dai ya maido da takunkuman da Amurka ta lafata wa Iran ko kuma a’a.

Sai dai masharhanta na ganin cewa, matakin maido da takunkuman ka iya sukurkuta yarjejeniyar nukiliyar ta Iran, abin da ake ganin ba zai haifar da da-mai- ido ba.