rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Korea ta Kudu Korea ta Arewa Amurka Nukiliya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Korea ta Kudu ta warware ama kuwwarta saboda zaman lafiya

media
Ana amfani da amsa kuwwar wajen ankarar da sojoji game da farmaki daga makociyar kasar AFP PHOTO/ KIM JAE-HWAN

Korea ta Kudu ta dakatar da ayyukan amsa kuwwar da ta sanya a kan iyakarta da Korea ta Arewa don ankarar da jama’a idan aka fuskanci farmaki daga makociyarta. Dakatar da aikin amsa kuwwar na zuwa ne a dai dai lokacin da ake shirin wata gagarumar tattaunawar zaman lafiya tsakanin kasashen a ranar juma’a mai zuwa.


Tun bayan yakin basasar  Korea da ya kai ga rabewarta zuwa gida biyu ne a shekarar 1950 zuwa da 1953 aka samar da amsa kuwwar wadda aikinta bai wuce ankarar da dakarun sojin Kudanci su kasance cikin shirin farmaki daga Arewaci ba,  zalika suma Arewacin.

Sai dai  wata sanarwar shalkwatar tsaron Korea ta Kudu ta ce, an dakatar da aikin amsa kuwwar don kawo karshen rikicin da ke tsakanin bangarorin biyu tare da tabbatar da zaman lafiya.

A Juma’a mai zuwa ne za a gudanar da gagarumar tattaunawar zaman lafiyar bayan da shugaba Kim Jong Un ya sanar da kawo karshen shirinsa na nukiliya.

Tuni dai shugaban Amurka Donald Trump ya ce matakin na Kim kan ajiye shirin makamin nukiliya shi ne kadai hanyar kawo karshen rikicin da ke tsakaninta da kasashen duniya, in da ya tsayar da ranar tattaunawar.

Ita ma dai Korea ta Arewan rahotanni sun bayyana cewa, tuni ta fara aikin warware amsa kuwwarta da ke kan iyaka don tabbatar da zaman lafiyar.