rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Libya Faransa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Khalifa Haftar ya koma Libya bayan jinya a Paris

media
Khalifa Haftar, kwamandan sojin gabashin Libya STR / AFP

Babban Kwamandan Soji da ke da karfin fada a ji a gabashin Libya, Khalifa Haftar ya koma Benghazi bayan shafe tsawon makwanni biyu yana jinya a birnin Paris na Faransa.


Jim kadan da saukarsa daga jirgin sama, Haftar mai shekaru 75 ya yi ta murmushi tare barkwanci a yayin mika gaisuwa ga tawagar manyan dakarun soji da dattawan da suka yi dandazo don tarbar sa a yammacin jiya Alhamis.

A jawabinsa da aka watsa ta kafar talabijin daga filin jiragen sama, Haftar ya tabbatar cewa yana cikin koshin lafiya.

Mahukuntan gabashin Libya dai, ba su fitar da hotuna ko kuma bayanai game da lafiyar Haftar a lokacin da ke jinyar a birnin Paris ba, lamarin da ya ruruta wutar cece-kuce game da halin da yake ciki da kuma makomar shirin raba madafan iko daidai wa daida tsakanin bangarorin da ke takun saka da juna a kasar.