rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Korea ta Kudu Korea ta Arewa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Trump na cigaba da shirin ganawa da Kim

media
Shugabanin kasashen Koriya ta Arewa da Amurka ®REUTERS/KCNA

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewar al’amura na tafiya daidai bayan tattaunawar da yayi da shugaban kasar Koriya ta Kudu Moon Jae-In dangane da shirin ganawar sa da shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa.


Trump ya bayyana haka ne ta kafar twitter cewar, yayi doguwar tattaunawa da shugaba Moon Jae-In, kuma komai na tafiya daidai, yayin da ake shirin sanya wurin taron da za suyi da kuma lokacin da za’ayi shi.

Shugaba Trump ya kuma ce ya tattauna da Firaministan Japan Shinzo Abe domin yi masa bayani kan halin da kae ciki.

Jiya juma’a ce shugaban Koriya ta Arewa da takwaran sa na kudu suka gudanar da wani taro mai dimbin tarihi, wanda shine irin sa na farko tun bayan yakin da suka gwabza shekaru 65 da suka gabata, inda suka yi alkawarin yin aiki tare.