Isa ga babban shafi
Iraqi

hukuncin daurin rai da rai kan wasu mata yan kungiyar Isil

Kotu a kasar Iraqi ta sanar da yankewa wasu mata 19 yan kasar Rasha hukuncin daurin rai da rai, saboda samun su da laifin shiga kungiyar IS.

Mutane sun taru a inda Mayakan ISIS suka tarwatse a Mosul na kasar Iraqi
Mutane sun taru a inda Mayakan ISIS suka tarwatse a Mosul na kasar Iraqi REUTERS/Stringer
Talla

Alkalin kotun dake shari’ar manyan laifufukan da suka hada da ayyukan ta’addanci, yace an samu matan ne da laifin taimakawa mayakan kungiyar.

Kotun ta kuma daure wasu mata 6 da suka fito ne daga Azerbaijan da wasu 4 daga Tajikistan.

Jakadan Rasha a kasar yace zasu tuntubi iyalan su domin shaida musu halin da ake ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.