rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Amurka Donald Trump Muhammadu Buhari Tattalin Arziki Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Najeriya da Amurka sun karfafa alakar tsaro da kasuwanci

media
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a lokacin da yake gaisawa da takwaransa na Amurka Donald Trump, a fadar White House, yayin ganawa da manema labarai. 30, Afrilu, 2018. REUTERS/Carlos Barria

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da takwaransa na Amurka Donald Trump bayanda ya fara ziyarar kwanaki uku a kasar.


Tattaunawar shugabannin biyu ta fi karkata ne akan batun yaki da ta’addanci, sai kuma fannin kulla alaka a fannonin zuba hannun jari da kasuwanci.

Yayinda suke jawabi ga manema labarai bayan ganawar da suka yi shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana gamsuwarsa da yadda Najeriya ke jagorantar yaki da ta’addanci musamman kungiyar Boko Haram.

Bayan tattaunawa kan Batutuwan tsaro da suka shafi tsaro, tattalin arziki da kuma yadda za’a shawo kan rikice-rikicen addini, a nashi bangaren shugaba Buhari yabawa goyon bayan da Amurka yi musamman game yerjejeniyar cinikin makmai da jiragen yaki don yakar ayyukan ta’adanci.

A watan Janairu na shekarar 2017 gwamnatin Barrack Obama, ta dakatar da batun saidawa Najeriya Jiragen yakin bayanda sojin kasar suka hallaka kimanin mutane 100 a wani sansanin ‘yan gudun hijira bisa kuskure a jihar Borno, yayinda sukai nufin kaiwa mayakank Boko Haram farmaki.

A fannin tattalin arziki kuwa,  shugaban Amurka Donald Trump ya yaba da rawar da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke takawa wajen yaki da cin hanci da rashawa da kuma inganta harkokin zuba jari a kasarsa.

A cewar Trump kokarin na shugaban Najeriya zai saukakawa 'yan kasuwar Amurka damar zuba jari, a kasar.