rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa Iran Birtaniya Jamus

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Faransa,Birtaniya da Jamus sun amince da karfafa yarjejeniyar nukiliyar Iran

media
Emmanuel Macron, Theresa May da Angela Merkel a zaman tattaunawa dangane da batun Nukiliyar Iran REUTERS/Francois Lenoir

Shugabanin Kasashen Faransa, Jamus da Birtaniya sun sake jaddada goyan bayan su kan yarjejeniyar nukiliyar Iran wanda suka ce itace hanya mafi inganci da za’a magance barazanar amfani da makamin daga kasar.


Firaminista Theresa May ta tattauna da shugaban Faransa Emmanuel Macron da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel inda suka bayyana goyan bayan su ga yarjejeniyar, da kuma tabbatar da cewar kasashen duniya sun hana Iran mallakar makamin.

Shugabannin uku sun ce akwai wasu batutuwa da yarjejeniyar bata kun sa ba da suke bukatar ganin an saka ciki, amma kuma hakan ba zai sa su janye goyan bayan su kan yarjejeniyar ba.

Shugabannin sun bayyana aniyar cigaba da tuntubar juna tsakanin su da Amurka domin magance shakkun da Amurka ke da shi kan shirin, da kuma barazanar da ake ganin Iran ke da shi a yankin Asia da kuma shirin kasar na makamai masu linzami.

A ziyarar da yake yanzu haka, sabon Sakataren harkokin wajen Amurka, John Bolton yace Trump bai yanke hukuncin watsi da yarjejeniyar baki daya ba.