Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa da Australia za su hana mamayar China a yankin Pacific

Kasashen Faransa da Australia sun lashi takobin hana duk wata kasa gudanar da mamayar yankin Pacific da India da ke a Nahiyar Asia. Shugabannin kasashen biyu ne suka gabatar da wannan kuduri, suna hannunka-mai-sanda ga kasar China da ake zargi da kokarin mamayen yankin na Pacific da India.

Emmanuel Macron shi ne shugaban Faransa na biyu a tarihi da ya taba kai ziyara Australia wadda ta taimakawa Faransar da dakarun soji a yakin duniya na daya da na biyu.
Emmanuel Macron shi ne shugaban Faransa na biyu a tarihi da ya taba kai ziyara Australia wadda ta taimakawa Faransar da dakarun soji a yakin duniya na daya da na biyu. AAP/Brendan Esposito/via REUTERS
Talla

A lokacin tattaunawar da shugabannin suka gudanar, Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya bayyana cewar kasashen biyu tare da kasar India mai bin turbar Dimokradiyya a yankin, na da ‘yanci da kuma damar hana kare yankin daga abinda suka kira mamayar da kasar China ke kokarin yi wa kasashen da ke shimfide a yankin.

Bayyana cewar muhimmin abu a wurinsu shi ne su tabbatar da ganin an samu daidaito na mallakar iyakokin kasashen da kuma ci gabansu, ba tare da an samu wata mamaya ta nuna fin karfi daga wata kasa da ke kallon kanta babbar yaya ba a yankin.

A baya-bayan nan dai kasar Australia na dada damuwa da yadda mamayar China ke karuwa zuwa yankunan kassahen, abinda a ganinsu, ka iya lalata kokarin da ake na samar da daidaito a tsakaninsu.

A watan da ya gabata ma an fidda rahoton da aka musanta daga bisani cewar kasar China ta kuduri aniyar kafa sansanin Soji na din din din a yankin Vanuatu, baya ga batun samar da Dallar Amurka biliyan1.78 kudaden tallafi da Chinar ta yi ga kassahen yankin na Pacific.

A tarihi shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron dai shine shugaba na biyu a Faransa da ya taba kai ziyara a Australia wadda a baya ta taimaka wa Dakarun kasar Faransa a lokacin yakin Duniya na 1 da na 2.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.