Isa ga babban shafi

"Mutane miliyan 7 suna mutuwa duk shekara a dalilin gurbatar iska"

Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya WHO, tace sama da kashi 90% na al’ummar duniya suna shakar gurbatacciyar iska, kuma hakan ke sanadiyyar mutuwar akalla mutane miliyan 7 a kowacce shekara.

Wata katafariyar masana'anta da ke fitar da hayaki a birnin Minsk, na kasar Belarus.
Wata katafariyar masana'anta da ke fitar da hayaki a birnin Minsk, na kasar Belarus. REUTERS/Vasily Fedosenko
Talla

Sabon rahotan hukumar ta WHO, yace kusan kowane bangare na duniya yana fama da matsalar gurbatar muhalli, amma matsalar tafi muni a yankunan da suke fama da talauci.

Binciken da hukumar ta gudanar, ya duba matsalar gurbatar muhalli ne a waje da kuma cikin gidaje.

Rahotan yace kashi 90 na masu mutuwa sakamakon cutar dake da nasaba da numfashi sun yawa a kasashe matalauta dake Asia da Afirka.

Rahotan yace shakar gurbatacciyar iskar yana haifar da matsalolin da suka kunshi, shanyewar jiki ko sankara, da kuma cutar nimoniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.